Zanga Zanga Ta Barke a Jigawa Kan Kwamishina, Matasa Sun Toshe Gidan Gwamnati

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. Jihar Jigawa - Masu zanga zanga sun yi awanya a gidan gwamnatin jihar Jigawa kan kwamishinan noma na jihar.

  • Masu zanga zanga sun toshe kofar gidan gwamnatin jihar Jigawa suna kalaman da suke nuna bacin rai tare da bayyana damuwansu
  • Matasa masu zanga zangar sun fito ne daga karamar hukumar Ringim, yankin da kwamishinan noma na jihar, Muttaka Namadi ya fito
  • Daya daga cikin wadanda suka shirya zanga zangar ya fadi dalilan da ya sa suka taru a kofar gidan gwamnatin domin nuna bacin ransu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Masu zanga zanga sun yi ƙawanya a gidan gwamnatin jihar Jigawa kan kwamishinan noma na jihar.

Mutanen sun fito ne daga karamar hukumar Ringim, yankin kwamishinan noma na jihar Jigawa, Muttaka Namadi.

Kara karanta wannan

Jigawa: masu zanga zanga sun kewaye gidan gwamnati, sun faɗi buƙatarsu

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa masu zanga zangar sun fito ne daga mazabun kananan hukumomin karamar hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin barkewar zanga zanga a Jigawa

Masu zanga zangar sun bukaci gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi da ya sauke kwamishinan noma na jihar.

Sun bayyana cewa sun bukaci haka ne domin kwamishinan, Muttaka Namadi bai tsinana musu komai ba a siyasance.

Daga ina masu zanga zanga suka fito?

Wani daga cikin jagororin masu zanga zanga, Abdullahi Muhammad ya ce sun fito ne daga mazabun Ringim 220.

Abdullahi Muhammad ya ce su ma yan jam'iyyar APC ne amma kwamishinan bai yi abin azo a gani ba a karamar hukumar Ringim kwata-kwata.

Jigawa-APC ta karbi masu zanga zanga

Daily Trust ta wallafa cewa masu zanga zangar sun dura gidan gwamnatin jihar Jigawa suna maganganun da suka nuna bacin rai.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanta ta 2, an gano halin da ake ciki bayan kifar da gwamnatin Bangladesh

Shugaban APC na jihar Jigawa, Aminu Sani ya karbi masu zanga zangar inda ya tabbatar da cewa zai isar da sakonsu ga gwamna Umar Namadi.

Gwamnan Jigawa zai ba monama tallafi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa za ta ba manoma mutum 30,000 tallafi saboda bunƙasa harkokin noma domin samar da abinci a jihar.

Majalisar zartaswar jihar ta amince da fitar da Naira biliyan 3.5 domin rabawa ga manoman a matsayin tallafin bunƙasa aikin noma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoNxhZhubmaykaO0onnZmqWgmV2prm6uwKuinmWRYreqs8CwmGajkaN6rMPApqCsoJmjrm65wK2YrJldqMKvedOoqqGdXZy2pa3NZp6wmZ2jrrW1jg%3D%3D

 Share!