- Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ya ce ba zai iya biyan ma'aikatan jiharsa sabon mafi karancin albashin N70,000 ba
- Gwamnan ya yi nuni da cewa ko tsohon albashin N30,000 sai jihar ta yi da kyar ake iya biya sakamakon matsin tattalin arziki
- A hannu daya, shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ya ce har yanzu Gombe ba ta karbi tirela 20 na shinkafa daga Tinubu ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gombe - A ranar Talata, gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya fadi cewa gwamnatinsa ba za ta iya biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ba.
Gwamna Inuwa Yahaya, ya yi magana a wani taro da shugabannin kwadago, kungiyoyin farar hula, da ’yan kasuwa gabanin zanga-zangar da za a yi a fadin kasar.
Ana tsaka da kuka da mulkin APC, 'yan majalisa 3 a Arewa sun sauya sheka zuwa daga PDP
"Ba zan iya biyan N70000 ba" - Gwamna
Jaridar Leadership ta ruwaito Gwamna Inuwa ya koka kan cewa cewa jihar Gombe na daya daga cikin jihohin da ke karbar mafi karancin kaso daga gwamnatin tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ba zan iya biyan mafi karancin albashin N70,000 ba, kuma ina zargin wasu jihohi da dama suna cikin wannan mawuyacin halin.”- Gwamna Inuwa Yahaya
Gwamnan, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ya ce samun kudi kadan ya sa jihar na fuskantar kalubale wajen iya biyan ma'aikata albashinsu.
Gombe ba ta karbi tallafin shinkafa ba
Gwamnan ya yi nuni da cewa hatta mafi karancin albashin N30,000 da aka amince da shi a baya, gwamnoni da dama na shan wahala kafin su biya.
Ya jaddada cewa yanayin tattalin arzikin da ake ciki a halin yanzu yana kara zama kalubale ga jihohi wajen aiwatar da sabon tsarin albashi, inji rahoton jaridar Premium Times.
NYSC: Tinubu zai ƙarawa matasa masu bautar ƙasa alawus? Abu 3 da ya kamata ku sani
Gwamna Inuwa ya kuma ce har yanzu Gombe ba ta karbi tirela 20 na shinkafa da gwamnatin tarayya ke rabawa jihohi ba, da nufin rage radadin da ‘yan kasar ke ciki.
An karawa ma'aikatan Gombe albashi
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Gombe ta amince da ƙara wa ma'aikatan jihar albashi domin rage masu radadin cire tallafin man fetur.
Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Inuwa Yahaya ta amince da ƙara wa kowane ma'aikaci a kowane mataki N10,000 a albashinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlmZYJzhJBmnrCZnaOur3nAqZpmsZFisKZ5wZpks5mZYra6rYyboLKZnmLAoq7Op2SmmZaeeqyt0ZqlnKGeYq6trsCsn6JlkpZ8